Tuesday, April 21, 2020

Samaila Isa Funtua ya yi fatali da mukamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Najeriya.


Tsohon minista a jamhuriya ta biyu, Alhaji Sama'ila Isah Funtua ya shawarci masu danganta shi da mukamin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da su kai kasuwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito an ambaci Funtua mai shekaru 78 daga cikin wadanda ake sa ran zasu maye gurbin marigayi Abba Kyari wanda ya rasu a dalilin cutar COVID-19 a ranar Juma'a.

Funtua, ya taba zama jami’in mulki a Katsina NA tsawon shekaru 7, ministan ruwa, kuma yana cikin mutanen da suka tsara daftarin kundin tsarin mulki a shekarar 1994-1995.

Shi ne mai kamfanin gine gine na Bulet, kamfanin mutum daya mafi girma a Najeriya da ta gina mafi kyawun gine ginen dake babban birnin tarayya Abuja, kuma babban dan jarida ne.

Don haka ya ce baya bukatar wannan mukamin saboda a cewarsa shi kan sa yana daukan mutane aiki a Najeriya, don haka ya girmi wani ya dauke shi aiki a wannan lokaci.

“Ni ma ina daukan ma'aikata aiki ne, don haka babu yadda za'ayi a dauke ni aiki. Ni fa minista ne a shekarar 1983, don haka wani mukami zai bani sha'awa yanzu? Na ji kunya da wata jarida ta danganta ni da wannan mukami saboda tsabar jahilci.” Inji shi.